Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Saki Alkali Janet Gimba A Kaduna, Sun Cigaba Da Garkuwa Da ‘Ya’yanta 3


Yan bindiga
Yan bindiga

Mijin alkaliyar Musa Gimba ya tabbatar da sakin na ta sai dai yace ana cigaba da yin garkuwa da ‘ya’yanta 3.

An saki Alkaliyar Babbar Kotun Shari’ar Gargajiya ta jihar Kaduna, Janet Gimba, wacce ‘yan bindiga suka sace tare da ‘ya’yanta 4.

Sai dai har yanzu ‘yan bindigar na cigaba da yin garkuwa da ‘ya’yanta 3.

Mijin alkaliyar Musa Gimba ya tabbatar da sakin na ta sai dai yace ana cigaba da yin garkuwa da ‘ya’yanta 3.

Ya bayyana cewar ‘yan bindigar na neman a biyasu kudin fansa na naira miliyan 150 cikin kwanaki 3, inda suka yi barazanar hallaka yaran matukar aka gaza biyan kudin.

A ranar 24 ga watan Yunin daya gabata ne aka sace alkaliyar dake aiki a babbar kotun shari’ar gargajiya dake yankin Sabon Tasha na jihar Kaduna tare da ‘ya’yanta 4, a gidansu dake Unguwar Mahuta ta karamar hukumar Chikun dake wajen birnin Kaduna.

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mansir Hassan ya bayyana cewar ‘yan bindigar sun hallaka babban dan alkaliyar mai shekaru 14 da haihuwa mai suna Victor Gimba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG