Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Atiku Ya Ce Kan Sace Mahaifiyar Rarara


Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya kwatanta matsalar garkuwa da mutane da ake yawan samu a kasar a matsayin wata alama da ke nuna gazawar shugabannin kasar.

Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023 ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

“Wadannan sace-sace na mutane da ake yi, na nuna gazawar shugabanninmu a fannin kare lafiyar al’uma.” In ji Atiku.

A cikin sanarwar, Atiku ya buga misali da sace tsohon shugaban ma’aikatan kamfanin wutar lantarki da gas, Mr. Takai Shamang mai shekaru 78 da ‘yan bindiga suka yi a jihar Kaduna.

A cewar Atiku, gabanin hakan, an sace Mai Shari’a Janet Galadima-Gimba a Kadunar wacce aka sako daga baya.

“Amma har yanzu ‘ya’yanta na hannun masu garkuwa da mutane wadanda suke neman a biya su miliyan 150 a matsayin kudin fansa.

“Kazalika a Katsina, an sace Hauwa Adamu mai shekaru 75, mahaifiya ga fitaccen mawakin Hausa Dauda Kahutu Rarara.”

A cewar Atiku, matsalar ta garkuwa da mutane na kara nuna irin mawuyacin halin da Najeriya ta shiga.

“Muna taya iyalan wadanda aka sace alhini da addu’a. Ina kuma kira ga hukumomin tsaro da su yi aiki tukuru domin ganin an sako su, amma su fi ba da karfi wajen tattara bayanan sirri.” Atiku ya ce.

Hukumomin Najeriya sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun kawar da matsalar ta tsaro ta hanyar daukan matakai daban-daban.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG