Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Jami’a A Katsina, Tare Da Yin Awon Gaba Da ‘Ya’yansa


MAlamin Jam'ia, Tiri Gyan
MAlamin Jam'ia, Tiri Gyan

‘Yan bindiga sun hallaka wani malami a jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma dake jihar Katsina.

An hallaka Dr. Tiri Gyan ne a sabon harin da ‘yan bindigar suka kai da sanyin safiyar yau Talata.

Wani shaidan gani da ido ya shaidawa tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho cewa, al’amarin ya faru ne da misalin karfe 1 da rabi na dare a gidansa dake karamar hukumar Dutsin-Ma ta jihar Katsina.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun mamaye unguwar da muggan makamai, suna harbin kan mai uwa da wabi, kana daga bisani suka yi awon gaba da 2 daga cikin ‘ya’yan malamin jami’ar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai yace nan bada jimawa ba rundunar zata fitar da cikakkun bayanai akan sa.

Dutsin-Ma na cikin kananan hukumomi 10 dake fama da hare-haren ‘yan bindiga kusan a kowace rana duk kuwa da kokarin gwamnatin Katsina da hukumomin tsaro ke yi na dawo da zaman lafiya a jihar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG