A safiyar Litinin din nan ne dai 'yan-uwan mutanen da 'yan-bindigan su ka sace su ka yi zanga-zanga a Abuja da Kaduna domin nuna damuwa game da cigaba da rike 'yan-uwan su da 'yan-bindigan ke yi a daji. Ana cikin wannan zanga-zanga sai ga labarin sakin mutane uku daga ciki kamar yadda Malam Abdul-Azeez Attah da ke da 'yan-uwa biyu a hannun 'yan-bindigan ya tabbatar.
Attah ya ce sakin mutane ukun ya biyo bayan sulhu ne da tattaunawa tsakanin 'yan-bindigan da kuma iyalan wadanda aka sako amma babu hannun gwamnati a ciki. Ya ce mahaifiyar shi wadda ke hannun 'yan-bindigan ta tsufa sosai amma ita har yanzu ba a sake ta ba.
Ku Duba Wannan Ma 'Yan Uwan Fasinjojin Da Aka Sace A Jirgin Kasa Na Kaduna Zuwa Abuja Sun Yi Zaman Dirshan Na Bayyana Bacin RaiBarrista Hasan Lawal Usman na cikin mutane ukun da 'yan-bindigan su ka sako su jiya Litinin da rana kuma ya ce dalilin sakin faifan bidiyon da aka nuna ana ta dukan su a karshen mako shine yadda gwamnati ta ki bari 'yan-uwan su su shiga daji don karbo su.
Ya ce duk da shakar iskar 'yancin sakin shi, har yanzu ya na cikin damuwa saboda halin da sauran mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja-Kadunan ke ciki a daji bayan kwashe watanni hudu.
Sakin wadannan mutane uku dai ya kai adadin wadanda aka sako zuwa mutane 23 sai dai kuma yanzu tattaunawar sakin mutanen ta koma tsakanin 'yan-bindigan da kuma iyalan wadanda ke hannun su a dajin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5