Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Wani Tsauni Muka Buya Kafin A Kawo Mana Dauki- Fasinjan jirgin Kasa Da Aka Kai Wa Hari A Hanyar Kaduna


Ana Dab Da Kamala Aikin Jirgin Kasa Daga Warri Zuwa Kogi
Ana Dab Da Kamala Aikin Jirgin Kasa Daga Warri Zuwa Kogi

Fasinjan ya ce zuwa yanzu, mutum 9 ne su ka rasa ransu ciki har da direban jirgin, inda wasu kuma su ka samu raunuka.

Daya daga fasinjojin jirgin kasan da barayin daji su ka kai wa hari kan hanyar Abuja zuwa Kaduna Abdulwabid Ahmad ya ce bayan harin sojoji sun zo inda su ka taimaka mu su su ka hau wani tsauni gabanin jigilar su a mota zuwa tudun mun tsira.

Abdulwabid Ahmad ya baiyana cewa bayan dasa nakiya da ta kayar da jirgin, barayin sun yi musayar wuta da jami’an tsaron da ke raka jirgin, inda su ka fi karfin su har su ka kutsa cikin jirgin su na harbe-harbe da kuma ya kai ga sace fasinjoji da dama.

Cikin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Cikin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.

Fasinjan ya ce zuwa yanzu an kirga mutum 9 ne su ka rasa ran su ciki har da direban jirgin, inda wasu kuma su ka samu raunuka.

Ahmad ya ce shi ma a karkashin kujera ya buya ya na addu’a har lamarin ya lafa bayan harbe wani fasinja a taragun da su ke ciki.

Haka nan ya ce barayin da motoci su ka zo su ka jide mutane su ka kutsa cikin daji.

Sojoji, a cewar fasinjan, sun bukaci fasinjojin da su kashe fitilar wayoyin su, da rage surutu har a samu a kubutar da su dsaga yankin mai hatsari.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG