'Yan Bindiga Sun Sace Mutane Da Dama A Kaduna

Yan Bindiga

Yan Bindiga

Sa'o'i kadan da sanar da kashe wani kasurgumin dan-bindigan da ya addabi mutane a yankin Kaya da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, wasu 'yan bindiga sun kai hari wani coci a Karamar hukumar Chukun, inda su ka sace sama da mabiya 40.

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna dai ta sanar da farma wasu 'yan bindigan da jami'an 'yan sandan su ka yi arba da su a kan hanyar Fatikan karamar hukumar Giwa, inda har su ka kashe wani kasurgumin dan bindiga daga ciki.

Sai dai kuma a rana guda wasu 'yan bindigan suka afkawa wani coci da ake kira Bege Baptist Church da ke kan hanyar Burukun karamar hukumar Chukun, inda su ka sace mabiya sama da 40.

Rabaren Joseph John Hayaf, shi ne shugaban kungiyar Kiristoci (CAN) a jihar Kaduna ya ce har zuwa daren ranar Litinin 'yan bindigan ba su kira waya ba, yana mai cewa an sako wasu daga cikinsu.

Hayaf ya ce matukar gwamnati da jami'an tsaro ba su tashi tsaye wajen kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a jihar Kaduna ba, to al'umomi za su ci gaba da shiga kuncin rayuwa da koma baya.

Ya kuma kara da cewa dawowar hare-haren 'yan bindiga zai iya maida hannun agogo baya, inda ya ce amfanin gwamnati samar da ingantaccen tsaro kuma idan ba tsaro to ba maganar ci gaba.

Amma duk kokarin neman mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ya ci tura saboda na tura mai sakon neman bayani kan wannan hari bai bani amsa ba, ko da yake kuma ya shedawa wata jarida cewa labarin harin bai zo musu ba.

A baya dai an dan sami lafawar hare-haren 'yan bindiga a wasu sassan jihar Kaduna kafin sake dawowar hare-haren cikin wadannan kwanaki, shi ya sa na nemi Sakataren kungiyar tsaffin jami'an tsaro ta Najeriya Dr. Auwal Abdullahi Aliyu, wanda ya ce wannan na da nasaba da maida hankali da jami'an gwamnati, da 'yan siyasa da ma jami'an tsaro su ka yi kan maganar mika mulki a karshen wannan wata na Mayu da mu ke ciki.

Dama kananan hukumomin Birnin Gwari, Chukun, Giwa, Igabi da Zangon Kataf ne su ka fi fama da hare-haren 'yan bindigar, sai dai kuma dab da lokacin zabe hare-haren sun yi sauki kafin sake dawowar su jifa-jifa daga baya.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Bindiga Sun Sace Mutane Fiye Da 40 A Kaduna.mp3