Duk da sanarwar da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi na kubutowar daliban makarantar Sakandiren gwamnati da ke Awon a Karamar hukumar Kachia, wasu kungiyoyi sun ce har yanzu fa iyayen daliban ba su gansu ba tukuna ko da yake sun ce da gaske ne sun kubuto.
A ranar uku ga wannan watan ne da 'yan-bindiga su ka sace daliban makarantar Sakandiren gwamnati dake Awon wanda bayan kwashe kwanaki goma sha biya a jiya Talata sai ga sanarwar gwamnatin Jahar Kaduna cewa dalibai takwas wadanda dukkan su mata ne sun kubuto da kan su.
Kungiyar Kiristoci ta kasa CAN, reshen jahar Kaduna ta ce labarin kubutowar daliban abun murna ne amma fa akwai wasu abubuwan lura masamman game da kusancin gurin da aka ajiye daliban da kuma kudanchin Kaduna.
Shugaban Kungiyar ta CAN, Rebaren Joseph John Hayaf ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara azama wajen kawo karshen hare-haren 'yan-bindiga a sassan jahar Kaduna don samarda ingantaccen tsarin tsaro.
Kungiyar al'umar kudanchin Kaduna wato SOKAPU kuwa cewa ta ce duk da ya ke ba ta shakkar kubutowar daliban amma fa har yanzu ba iyayen su ma ba su san ina aka kai su ba.
Mai-magana da yawun kungiyar, Mr. Luka Biniyat ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa duk kokarin kungiyar na sanin takamaiman inda aka ajiye daliban ya gagara amma labarin kubutowar su gaskiya ne.
Masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya kuwa gani su ke yi akwai yuwuwar 'yan-bindigan da su ka sace daliban ba su kammala shirin boye daliban ba ne har Allah Ya basu ikon gudowa amma ya ce akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye don kawo karshen matsalar baki daya.
Sanarwar kubutowar daliban makarantar Sakandiren gwamnatin da kwamishinan tsaro ya fitar dai ta ce daliban sun ci doguwar tafiya ta kwanaki kafin jami'an tsaro su kai mu su dauki, a saboda haka yanzu haka su na hannun hukuma don duba lafiyar su kafin damkawa iyayen su su.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara: