Cikin daren Asabar wayewar garin jiya Lahadi ne dai 'yan-bindigan su ka afkawa garin Runji dake karamar hukumar Zangon Kataf inda su ka kashe mutane da dama. Shugaban karamar hukumar, Mr. Francis Sani ya ce har yanzu ba a gama kididdige adadin wadanda 'yan-bindigan su ka kashe ba.
Shugaban karamar hukumar ya ce su lallashin mutane ne yanzu cewa su yi hakuri kada su ce za su dauki matakin ramuwa domin ana bincike.
Sai dai kungiyar al'ummar kudancin Kaduna wato SOKAPU ta ce mutanen da aka kashe sun haura 30. Mai magana da yawun kungiyar, Mr. Luka Biniyat ya ce a gaban shi aka binne gawawwakin sama da mutane 30 wasu ma duk an kone su.
A cewar Biniyat wannan harin yayya ne kuma cikin wata daya da ya wuce an kai irin wannan hari har guda uku a wurare mabanbanta a kudanchin Kaduna.
Shugaban Kungiyar Fulani wato Miyatti Allah a jahar Kaduna, Alh. Haruna Usman ya ce idan irin wannan hari ya afku to a bar jami'an tsaro su yi bincike.
Ya ce akwai alamun ramuwar gayya saboda ko ranar Juma'a an kashe yaro mai kiwo kuma aka zubawa shanu guma har aka kashe wasu.
Karamar hukumar Zangon Kataf dai na kan gaba cikin kananan hukumomin kudancin Kadunan da ke fama da hare-haren 'yan-bindiga, abun da ya sa gwamnati ta girke bataliyar jami'an tsaro a yankin don kawo karshen matsalar tsaro sai dai kuma wasu na ganin har yanzu da sauran rina a kaba game da wannan matsala ta hare-haren da ke da jibi da ramuwa.
Ga rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna a Najeriya: