Rahotanni daga yankin Kumbashi na karamar hukumar Mariga da kuma Kafinkoro na karamar hukumar Paikoro a jihar Neja, sun nuna cewa maharan sun share yinin ranar Laraba da ta gabata suna tafka ta’asar su a wadannan yankuna.
Wani mazaunin garin Kumbashi da ya nemi a sakaya sunan shi, ya ce yanzu haka sun tsere daga garin kuma suma Allah ne ya kiyayesu domin suna bayansu suna gudu.
Shima wani mazauni garin Kafinkoro ya tababtar wa da Muryar Amurka cewa ‘yan bindigar sun kai hari garin, kuma yanzu haka babu jami’an tsaro a garin.
Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, lokacin da yake zantawa da mataimakin Sufeto Janar na Yan sandan Najeriya, AIG Aliyu Garba, ya ce “Da safiyar nan ‘yan bindigar suka fito da ya wa a shiyar Kumbashi, kuma sun dauki sa’o’i suna musayar wuta da jami’an tsaronmu, abun takai cima daya daga cikin kwamandojinmu ya rasa ransa, kuma ma har ya zuwa yanzu ba mu gama tantace adadin wadanda suka mutu ba daga duka bangarorin biyu.”
Mataimakin Sufeton ‘Yan sandan, AIG Aliyu Garba, ya ce ya shigo jihar Neja ne domin tabbatar da ingantuwar tsaro kuma suna hada hannu da sauran jami’an tsaro domin magance bata gari.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5