'Yan Bindiga Sun Kashe Ma'aikatan Jinkai Faransawa Shida a Nijar

Wasu jami'an wanzar da zaman lafiya na rundunar sojojin Tafkin Chadi-Nijar

Wadansu ‘yan bindiga sun hallaka ma'aikatan jinkai faransawa da wasu ‘yan rakiyarsu ‘yan Nijar a garin Koure dake tazarar kilomita 59, kudu maso gabashin birnin Yamai *GARGADI: Ya yiwu hoton da ke cikin rahoton ba zai yi wa mai karatu kyaun gani ba*

Tun farko jami'ai sun bayyyana faransawan a matsayin 'yan yawon bude ido, kafin daga baya, ministan tsaro na Jamhuriyar Nijar Lamarin ya faru ne a tsakanin karfe 11 zuwa 12 na ranar lahadi 9 ga watan Agusta a kewayen kauyen Koure na yankin Tilabery dake matsayin wani gandun daji mai jan hankulan masu yawon bude ido daga sassan duniya saboda garken rakuman dajin da ke rayuwa a wannan wuri shekaru aru aru.

Rahotanni na nuni da cewa, faransawa 6 da ‘yan Nijer 2 ne suka gamu da ajalinsu lokacin da wasu mutane akan babura suka bude masu wuta suka kuma kona motar da 'yan yawaon bude idon da jagororin su suke ciki, da aka bayyana cewa motar mallakar kungiyar da ake kira ONG ACTEL ce.

A cikin hirarsu da Sashen Hausa, gwamnan yankin Tilabery Tidjani Ibrahim Katchalla ya tabbatar da faruwar wannan lamari.

Hukumomin sun bayyana cewa nan da nan aka baza jami’an tsaro domin cafko wadannan mahara sai dai kuma wasu mazauna birnin Yamai na matukar mamakin yadda harin ya wakana a yankin da ake ganin ya fi ko' ina tsaro a Jamhuriyar Nijar.

Ganin yanayin da aka shiga a yankin Tilbery ya sa ma’aikatar ministan cikin gidan Jahuriyar Nijar a shekarar 2019 ta gargadi kungiyoyi masu zaman kansu su kiyayi zagaya wannan yanki mai makwaftaka da kasahen Mali da Burkina Faso ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba, saboda haka ake ganin rashin mutunta wannan tsari ya yi tasiri wajen baiwa ‘yan bindiga damar kai wannan hari na jiya lahadi.

Wannan na faruwa ne kwana daya kacal bayan da jami’an tsaro suka murkushe wani harin da ‘yan bindiga suka shirya kaiwa a karkarar Galmi dake yankin Tahoua inda rahotanni ke cewa an kashe dan bindiga daya tare aka kuma cafke wasu daga cikinsu, yayinda aka bi sawun wasu 2 da suka ranci ta kare.

Saurari rahoton da wakilin muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma ya aiko mana ta sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Bindiga Sun Kashe Faransawa Shida 'Yan Yawon Bude Ido a Nijar-2:40"