Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Niger: Wasu Manyan Kungiyoyin Afrika Sun Tattauna Akan Batun Tsaro


Wasu jami’an kungiyar tarayyar Afrika ta AU, da ECOWAS, da kungiyar dakarun G5 Sahel sun gudanar da wani taro a yammacin jiya litinin a birnin Yamai na jamhuriyar Nijer domin nazarin hanyoyin girke sojoji 3000 na rundunar da kungiyar AU ta yi alkawalin aikewa a yankin Sahel, a ci gaba da daukar matakan tunkarar kungiyoyin ta’addancin arewacin Mali.

A taron shugabanin kasashe da na gwamnatocin Afrika da aka yi a ranakun 9 da 10 ga watan Fabarairun da ya gabata ne kungiyar AU ta yanke shawarar ba kungiyar G5 Sahel gudunmuwar sojoji 3000 domin tunkarar matsalar ta’addancin da ta addabi kasashen yankin na sahel, mafari kenan aka shirya wannan taro na hadin guiwar AU, da G5 Sahel, da CEDEAO da nufin nazari akan hanyoyin da zasu bada damar zartar da wannan kudiri a cewar Ministan Tsaron Nijer Issouhou Katambe.

Ministan ya kuma ce batun inganta rayuwar al’umomin da wannan yaki ya jefa cikin halin tagayyara wata matsala ce ta dabam da ya kamata a dauka a matsayin wani bangare na hanyoyin magance matsalar ta’addanci a Sahel.

Kwamishinan kungiyar tarayyar Afrika mai kula da sha’anin tsaron Nijar, Ismael Chargui, ya bayyana cewa, idan kasashe suka ci gaba da hada dabaru da karfinsu a wuri guda, tabbas za a ba wannan yanki da ma Afrika gaba daya damar murkushe matsalar ta’addanci, hakan kuma zai taimaka a sami farfadowar al’amura a wannan yanki.

To amma jami’in kungiyar AU ya jaddada matsayin wannan kungiya wadda ta sha nuna bukatar daukar matakan warware rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a Libya, musamman abinda ya shafi tilasta wa bangarori mutunta takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Libya akan maganar makamai kamar yadda aka tsayar a taron Berlin na baya-bayan nan.

A karshen taron na wuni guda, sakataren kungiyar G5 Sahel, Maman Sambo Sidikou, ya gabatar da shawarwarin da shugabannin suka yi akan bukatar kafa wani kwamitin hadin gwiwa mai alhakin duba hanyoyin hanzarta girke dakarun rundunar kungiyar ta AU a yankin Sahel, yayin da taron ya gano bukatar matsa kaimi domin tattaro kudaden daukar dawainiyar ayyukan sabuwar rundunar mai askarawa kimanin 3000.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG