Ministar tsaron kasar Faransa, Florence Parly, ta bayyana shirin aika karin wasu dakarun Faransa 600 zuwa Yankin Sahel domin karfafawa askarawan kasar gwiwa da ke tafka yaki da kungiyoyin ta’addancin da suka addabi jama’a akan iyakokin Nijar da Mali, da kuma Burkina Faso.
Sojoji 220 ne a taron birnin Pau aka kudiri aniyar karawa akan sojoji 4500 da Faransa ta girke a Yankin na Sahel da sunan yaki da ta’addanci.
Amma lura da tsanantar al’amura ya sa shugaba Emmanuel Macron kara yawansu zuwa 600 inji wata sanarwar da ministar tsaron kasar Florence Parly ta fitar a ranar 2 ga watan nan na Fabrairu.
Sanarwar ta kara da cewa akasarin wadannan dakaru 600 za a girke su ne akan iyakokin Mali da Nijar, da kuma Burkina Faso.
Sai dai akwai wadanda suka nuna shakku game da matakin kara sojojin kasashen waje a Yankin Sahel.
Wasu kuma na ganin zai inganta yanayin rayuwa da taimakawa wajen kawo karshen ta'addanci.
Sanarwar ma’aikatar tsaron kasar ta Faransa ta yi nuni da cewa nan da kwanaki kadan ne karin sojojin za su isa Yankin Sahel domin soma aiki gadan-gadan.
Da ma a watan Disamba 2019 ne shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya jaddada bukatar samun karin sojin waje a kasashen Sahel domin fatattakar kungiyoyin ta’addancin da suka addabi wannan Yanki.
A saurari rahoto cikin sauti daga birnin Yamai.
Facebook Forum