Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Michael Abattam, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da safiyar Juma'a, ya ce harin ya auku ne da yammacin jiya Alhamis.
Ana dai zargin cewa maharan da suka zo makare cikin motoci da babura da dama, mambobin kungiyar yan awaren Biyafara da ke fafutukar kafa kasarsu da kungiyar tsaron kudancin kasar wato ESN ne, a cewar Abattam.
A cikin sanarwar, Abattam ya ce "a ranar 21 ga watan Oktoba da mu ke ciki da misalin karfe 6 da 44 ne wasu 'yan bindiga dauke da makamai da ake zargin mambobin kungiyar IPOB da ESN ne suka afkawa ofishin 'yan sanda dake Isiala Mbano a cikin motoci kusan biyar da babura uku."
Ya ci gaba da cewa "maharan sun jefa bama-baman kwalbar man fetur a kan rufin ginin da aka riga aka lalata a lokacin zanga-zangar EndSARS, kuma suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi" kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.
Jami'an 'yan sandan da ke aiki a yayin harin sun mayar da martani ta hanyan musayar wuta da batagarin inda suka fafata da su matuka kuma sun sami nasarar fatattakar su, lamarin da ya sa suka fara tserewa cikin motoci da baburan da suka zo da su.
Haka kuma, Abattam wanda ke zaman babban jami’i a aikin 'yan sanda, ya bayyana cewa jami'ansa da suka fafata da maharan sun tabbatar da cewa ba wani makami da maharan suka sami kwacewa a lokacin harin, kuma an kashe gobarar da ta tashi sakamakon bama-baman man fetur daga bisani, duk da cewa ta haifar da lalacewar ginin.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta garzaya da daya daga cikin jami’anta da ya sami raunin harbin bindiga zuwa wani asibiti da ke kusa don kula da shi, in ji sanarwar.
Abattam ya ce tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta tura jami’anta domin farautar maharan domin kama su da kuma karfafa matakan tsaro a yankin.
A yayin mayar da martanin, kwamishinan ‘yan sanda na Imo, Rabiu Hussaini, ya yaba da kokarin jami’an ‘yan sandan yankin saboda jajircewar su, sannan ya bukace su da su ci gaba da ba da himma wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Rabiu ya kuma mika godiya ga mazauna yankin saboda goyon bayan da suke ci gaba da ba su sannan ya roke su da su ci gaba da yin aiki tare da 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro don yakar laifuka da kare ofisoshin' yan sanda ta hanyar kawo bayanan sirri da za su taimakawa aikin ‘yan sandan.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da wadanda ake zargin mambobin kungiyar IPOB da ESN ne suke kai hari kan ofishin din yan sanda a jihohin kudancin kasar.