Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kungiyar IPOB Ne Suka Kashe Dr. Akunyili - Mefor


'Yan Kungiyar Fafukar Kafa Kasar Biafra IPOB.
'Yan Kungiyar Fafukar Kafa Kasar Biafra IPOB.

Duk da yake dai ba’a kai ga kama wadanda ke da hannu akan kisan ba, babban tsohon na hannun daman Nnamdi Kanu, Uche Mefor, ya bayyana kisan da cewa aiki ne na baya-bayan nan na kungiyar ta IPOB, zargin da kungiyar ta musanta.

Tsohon na hannun daman shugaban kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biyafara Nnamdi Kanu, wato Uche Okafor-Mefor, ya zargi ‘yan kungiyar ta IPOB da kisan Dr. Chika Akunyili.

Ita dai IPOB ta nesanta kanta da wannan kisa.

An bindige mijin na tsohuwar shugabar hukumar NAFDAC Farfesa Dora Akunyili har lahira, a yayin da yake kan hanyar dawowa daga halartar wani taron karama matarsa, da jami’ar Nsukka ta shirya a Onicha.

Dan marigayin, Obumneme, ya ce ‘yan bindigar sun budewa motar mahaifin na shi wuta ba kakkautawa, “inda suka kashe shi tare da direbansa, da kuma jami’in dan sandan da ke tare da shi.”

Dr. Chike Akunyili
Dr. Chike Akunyili

Duk da yake dai ba’a kai ga kama wadanda ke da hannu akan kisan ba, babban tsohon na hannun daman Nnamdi Kanu, Uche Mefor, ya bayyana kisan da cewa aiki ne na baya-bayan nan na kungiyar ta IPOB.

Mefor wanda a da babban jigo ne a kungiyar IPOB amma ya sauya tunani daga manufofin Nnamdi Kanu, ya wallafa wani dogon rubutu a sanannen shafinsa na Facebook, inda ya ci gaba bayyana ayukan ta’addanci da ya zargi kungiyar ta IPOB da aikatawa.

Ya ce kungiyar ce ke da alhakin ta’azzarar rashin tsaro da kisan jama’a a yankin Kudu maso gabas da sunan fafutukar neman ‘yanci.

Mefor ya kara da cewa “wannan ba yakin neman ‘yanci ba ne, aiki ne dai kawai aka kaddamar na kisan ‘yan kabilar Igbo da basu-ji-ba basu-gani-ba da sunan fafutukar neman ‘yanci.”

Uche Okafor-Mefor, Tsohon na hannun daman Nnamdi Kanu
Uche Okafor-Mefor, Tsohon na hannun daman Nnamdi Kanu

Dan gwagwarmayar ya kuma bayyana takaici akan yadda shugabannin yankin na kudu maso gabas, kama daga gwamnoni, shugabannin al’umma da na addini har ya zuwa shugabannin kasuwanci, suka yi gum da bakinsu akan “munanan ayukan” kungiyar ta IPOB, da ya ce sun karya dokokin yankin, da na kasa, da ma na kotun kasa-da-kasa ta ICC.

Ya bayyana shirun da shugabannin suka yi da cewa tamkar suna goyon bayan ayukan kungiyar ne, a yayin da ko wadanda suka yi yunkurin yin magana, ba za su iya fayyace gaskiya kan lamarin ba.

Mefor ya kara da cewa ba yadda za’a yi nasarar samun ‘yanci ta hanyar tashin hankali da daukar makamai, wanda ya ce sun dade da suka yi gargadi kan barin makamai su yawaita hannun jama’a a yankin, domin kuwa hakan zai haifar da rashin bin doka da yawaitar kungiyoyin ‘yan ta da kayar baya da za su addabi al’umma.

Sai dai darektan yada labaran kungiyar ta IPOB Emma Powerful ya nesanta kungiyar da kisan Mista Akunyili, inda ya yi zargin cewa “wadanda suka kashe matarsa, su ne suka kashe shi,” kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ana ci gaba da samun karuwar kalubalen tsaro a yankin na kudu maso gabas, a yayin da ‘yan kungiyar ta IPOB suke ci gaba da tsaurara dokar hana fita a wasu kebantattun ranaku, a yayin da kuma ake zarginsu da kai hare-hare kan duk wani dan yankin da ke kalubalantar tsarin tafiyar kungiyar.

XS
SM
MD
LG