Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Anambra: Za A Tura ‘Yan Sanda Dubu 34, Jirage Uku


'Yan sandan Najeriya (Facebook/NPF)
'Yan sandan Najeriya (Facebook/NPF)

A kwanakin baya hukumar zabe ta INEC ta nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a jihar, inda ta yi kira ga hukumomi su dauki mataki gabanin zaben.

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya ce ‘yan sanda dubu 34, 587 za a tura jihar Anambra gabanin zaben gwamna da za a yi a jihar.

A ranar 6 ga watan Nuwamba za a gudanar da zaben na Anambra wacce a baya-bayan nan take fama rigingimu masu nasaba da ‘yan kungiyar ‘yan aware ta IPOB da hukumomin kasar suka ayyana a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Sufeton ‘yan sanda ya bayyana wannan shiri ne yayin wani taro na musamman da ya yi da kwamishinoninsa a Abuja kamar yadda rahotanni suka nuna.

Baya ga dubban jami’an da za a tura, Alkali Baba ya ce za a tura jirage masu saukar ungulu guda uku domin yin shawagi a ranar zaben.

A kwanakin baya hukumar zabe ta INEC ta nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a jihar, inda ta yi kira ga hukumomin su dauki mataki gabanin zaben.

Wannan mataki da Sufeton ya sanar na zuwa ne kasa da mako biyu bayan da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ce mai yiwuwa a ayyana dokar ta-baci a jihar ta Anambra, kalaman da ba su yi wa gwamna Willie Obiano dadi ba.

XS
SM
MD
LG