Bayanai daga Yankin Bassa ta karamar Hukumar Shiroro na nuna cewa da safiyar ranar Alhamis din nan maharan suka aukawa wannan yanki,
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunanshi yace daga cikin mutane biyu da aka kashe jami'an tsaro ne na 'yan banga, sannan yace daga ranar Lahadin da ta gabata zuwa yanzu, sama da mutane 13 maharan suka kashe tare da yin Garkuwa da kimanin Mutane 40 a wannan yankin.
Shugaban karamar hukumar Shiroron, Hon. Akilu Isyaku Kuta yace yankin na Shiroro ya na cikin tashin hankali domin kuwa yanzu haka, mayakan Boko Haram suna dasa bama-bamai a hanya.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani karin haske daga rundunar yansanda ta jihar Neja akan wannan sabon hari domin kuwa kokarin samun kakakin 'yan sandan, Wasiu Abiodun yaci tura,
Amma Kwamishinan Kula da Harkokin Tsaron cikin Gida na jihar Neja Janaral Bello Abdullahi Muhammad mai ritaya ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace gwamnati na kokarin tabbatar da tsaro a wannan yanki.
Fatar Mutanen wannan yanki dai shine kara jibga jami'an tsaron sojoji a wannan yanki domin samun saukin wannan lamari.
A saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5