Ta’annatin balle gidan daurarru ko gyaran hali a Najeriya, musamman ma a yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya, al’amari ne da kusan ke aukuwa a kai a kai.
A yau ne rundunar tsaron ‘yan sandan Najeriya ta jahar Imo ta bada sanarwar cewar, wasu ‘yan bindiga da ta ce ‘yan IPOB ne ma su rajin kafa sabuwar kasa ta Biafra, sun kai hari kan wani gidan gyaran hali na wucin gadi da ke shiyyar Okigwe a jahar da yammacin jiya, inda kuma bayan harbe jami’in tsaro daya, ‘yan bindigar sun bada dama ga daurarrun su tsere, kuma kawo yanzu, babu tartibin yawan daurarru da su ka gudu, sai dai wasu alkaluma na nuna cewar daurarru bakwai ne su ka tsere.
Bayan dai maharan sun yi ta’adi a wannan gidan gyaran hali, wadda na wucin gadi ne da ke wata katafariyar gona a garin na Okigwe, an nunar sun nufi gidan wani dan majalisar dattawa, inda nan take su ka harbe jami’in tsaron ‘yan sanda da ke aiki a gidan har lahira.
Da ya ke tsokaci kan lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jahar ta Imo ya ce gidan gyaran hali na jahar Imo na da wani gidan daurarru na wucin gadi a garin Okigwe, wanda daurarru a ke kaiwa da su ke gab da gama wa’adinsu na zaman gidan gyaran hali, akwai kuma wata katafariyar gona da a kan sa su aiki, kuma nan ne ‘yan bindiga su ka kai hari, ina jin daurarru 7 ne su ka samu tserewa bayan yin awon gaba da jami’in gidan daurarrun da yan bindiga su ka yi kuma mu na zargin yan kungiyar IPOB ne.
Sun dai yi awon gaba da makamai da harsasai, ko da ya ke fadin cikakken bayani kan haka, sai daga jami’an na gidan gyaran hali, domin sanin yawan makamai da harsasai da ‘yan bindiga suka ka kwashe.
Rundunar ta ‘yan sandan jahar ta Imo dai ta ce ta kai ga kama wasu daga cikin maharan.
Sau tari dai in hari irin wannan ya auku a yankin, tare kuma da zargin ‘yan IPOB din, kungiyar ta kan yi wuf ta musa.
Peter Chukwu, wani dan kungiyar ta IPOB, ya ce "a matsayi na na cikakken dan kungiyar IPOB, na sani cewar a kwai kiyayya ta musamman tsakanimmu da jami’an tsaro, dan haka ko yaya a ka samu kai wani hari a yankin, za su fito su ce mu ne, domin kawai su bata mana suna a ciki da wajen Najeriya."
Alkaluma dai sun nuna yadda ‘yan bindiga a musamman yankin Kudu Maso Gabashin na Najeriya su ka maida balle gidan yari kamar wasa. Na baya-baya kafin na yammacin jiya ma wani babban batu ne har yanzu, shi ne na yadda ‘yan bindiga da su ma a ke zargin ‘yan kungiyar ta IPOB ne su ka balle gidan gyaran hali na birnin Owerri a jahar ta Imo a shekarar 2021, inda kuma su ka fidda daurarru kimanin 1,844,wanda kuma da damansu ba a kai ga sake kamo su ba har yau har gobe.
Saurari rahoton Abubakar Lamido Sokoto:
Dandalin Mu Tattauna