Kudirin, wanda ‘yan majalisar 13 suka gabatar, ya samu goyon baya daga galibin mambobin majalisar wakilan wadanda suka yi amanar cewar za’a iya take fargabar da ake da ita na kada gwamnonin jihohi su yi amfani da damar wajen danne ‘yan adawa domin shawo kan matsalar tsaron dake addabar kasar.
A makon daya gabata, Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin Najeriya 36 suka tattauna akan kirkirar ‘yan sandan jihohi a matsayin hanyar magance matsalolin tsaro irinsu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga da suka zamo ruwan dare a Najeriya.
Batun ‘yan sandan jihohi ya jima yana haifar da cece kuce a Najeriy tun a majalisa ta bakwai saidai har yanzu ba’a kai ga kammala yi masa kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar ba.
A baya bayan nan gwamnonin jam’iyyar PDP suka jaddada matsayarsu akan batun kirkirar ‘yan sandan jihohi, a matsayin hanyar shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro, inda suka koka akan cewar Najeriya ta kama irin tafarkin da kasar venezuela ke kai na rudani.
Haka suma, kungiyoyin al’ummomi irinsu Afenifere na Yarbawa da Ohanaeze Ndigbo na Igbo da Middle Belt Forum ta kabilun tsakiyar Najeriya da kuma na Dattawan Arewa, ya sha yin kira akan kirkirar ‘yan sandan jihohi a matsayin hanyar magance dimbin matsalolin tsaron dake kara addabar Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna