Da asubahin yau litini ne lamarin ya faru kan mutanen da basa dauke da makamai kwanaki kadan bayan jihar Filato ta kafa dokar hana yawo daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe a karamar hukumar Bassa, biyo bayan yawaitar kashe-kashen da ake yi a yankin.
Mai ba gwamnan jihar Filato shawar kan harkokin yada labarai Mr Dan Manjan, ya ce lamarin ya kasance abin takaici kwarai saboda dumbin rayukan da ke salwanta a wasu sassan jihar.
Shugaban matasa kabilar Irigwe, Ayuba Chinge, ya bayyanawa wakiliyar sashen Hausa na Muryar Amurka Zainab Babaji cewa mutanen da aka hallaka na zama a wata makarantar Firame ne karkashin kulawar wasu sojoji, kawo yanzu mutane ashirin da bakwai suka hallaka, wasu da dama kuma na kwance a asibiti.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Ummar Dakare, ya bayyana cewa babu hannun Fulani a cikin lamarin kuma ya yi kira ga daukacin Fulanin yankin da kada su dauki doka a hannunsu, su kasance masu biyayya ga gwamnati.
Daga jihar Filato, Zainab Babaji ta aiko mana da cikakken rahoto.
Your browser doesn’t support HTML5