Ranar Lahadin jiya ce “Ranar Wanke Hannu Ta Duniya” wanda a dalilin haka gwamnatin jihar Bauchi ta kira taron manema labarai da zummar bayyanawa duniya irin hobasar da ta yi kan tsafta.
Babban sakatare na Ma’aikatar Samar Da Ruwa Da Kula Da Tsaftar Jama’a, Alhaji Garba Magaji, ya bayyana irin kokarin da gwamnatin ijhar ta yi domin karfafa tsafta da samar da makewayi a kananan hukumomi guda takwas.
Yace a sanadin wannan hobassar, yanzu ana samun raguwar bullar cutar kwalara a jihar.
Alhaji Garba Magaji yace kafin su fara wannan shirin na musamman a can baya kowace damina akan samu barkewar cutar kwalara a yankunan, amma yanzu lamarin ba haka yake ba. Dalili ke nan da gwamnati ta mayar da hankalinta kan samar da ruwa da tsaftace muhalli, inji shi.
Wakilinmu dake jihar Bauchi Abdulwahab Muhammad ya zagaya cikin babban birnin jihar, Bauchi, domin ya ji tasirin wanke hannu a wurin jama’a.
Wadda ya fara zantawa da shi ta ce wanke hannu na cikin muhimman abubuwan da ya kamata a dinga yi domin kada a ci abinci da kazanta mai dauke da kwayoyin cuta.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani
Facebook Forum