Dr Ibrahim Ibrahim wanda ya zanta da muryar Amurka dangane da bukukuwan ranar ilimin ‘yaya mata na duniya da akayi a makon jiya yace Masar da Najeriya na nazarin yin aiki tare domin amfanar juna a fannonin ilimi daban daban, a banagren ilimin ‘yaya mata dana kiwon lafiyar bil’dama.
Ya kuma bayyana cewa hadin gwiwar tsakanin Najeriya da Masar zai maida hankali ne wajen musayar ra’ayi da fasaha kan hanyoyin warware matsaloli da kalubalen kasashen biyu a kowane fagen ilimi, musamman la’akari da cewa, Najeriya, nada Muradin karfafa fannin ilimin kimiyyar kiwon lafiya da sha’anin harhada magunguna.
Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da cibiyar nazarin jinsin dan'adam ta Jami’ar Bayero Kano, ta shirya taron fadakar da iyaye kan muhimmancin ilimin mata a karshen mako wadda domin dacewa da bikin ilimin ‘yaya mata na duniya da akayi a makon jiya.
Shi kuwa Dr Maikano Madaki na sashin nazarin halayyar dan'adam cewa ya yi rashin bada ilimi ga yara musamman ‘ya'ya mata na haifar da fitina a cikin al’uma.
Daga Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana da wannan rahoto.
Facebook Forum