Dubban jama’a ne dai rikicin Boko Haram ya tilastawa gudun hijira a ciki dama wajen Najeriya, baya ga wadanda aka kashe, musamman a jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe, dukkansu a arewa maso gabashin kasar.
To sai dai kuma kawo yanzu tuni lamura suka fara komawa daidai a wadannan yankunan da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram. Kuma sakamakon wannan kwanciyar hankalin ne ma yasa yanzu Hukumar Zabe ta Najeriya ta soma gudanar da aikin sabunta katin zabea yankunan.
Alal misali,a jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da balahirar Boko Haram din tafi shafa, yanzu haka aikin sabunta katin zabe ya soma samun nasara.
Barr.Kassim Gana Gaidam dake zama kwamishinan zabe a jihar yace, biyo bayan taron masu ruwa da tsaki a wadannan yankuna na kananan hukumomi bakwan da a baya suka fada hannun yan Boko Haram, yanzu haka aikin sake sabunta rajistan zaben na gudana inda ya bada misali da na karamar hukumar Madagali, inda har yanzu ake fama da burbudin yan Boko Haram.
Bincike na nuna cewa shi wannan aiki na sabunta katin zaben ba zai samu nasara ba muddin jama’a basu koma yankunan nasu ba, inda Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya wato NEMA ta dukufa wajen samar da cimaka da zimmar kara kaimi ga wadanda suka koma.
Bashir Garga, wanda shine jami’in hukumar ta NEMA mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, yace sun raba kayakin cimaka a daukacin kananan hukumomin da aka koman.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum