Wasu shugabannin kasashen Afirka da manyan ‘yan kasuwa sun bukaci kawo karshen anfani da bizar shiga kasashen nahiyar ta Afirka domin saukaka zirga zirga da kasuwanci tsakaninsu.
A taron da suka gudanar a lagos dake Najeriya domin kafa wata kungiyar habaka harakokin kasuwanci mai suna “Afro Champions Club”, jagoran kungiyar kuma attajiri mafi arziki a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana dalilin kafa kungiyar.
A cewarsa, suna so ne su jawo manyan kamfunan Afirka dake sarrafa kayayyakin da za’a iya kaiwa kasashen waje, ba ma Afirka ba kawai, domin a zauna dasu da gawamnati. Manufar ita ce a samar da hanyoyin da za’a taimaka masu domin su ba mutane aiki. Dangote yace suna son su dinga yin kasuwanci tsakaninsu maimakon kasashen wajen Afirka. Kawo yanzu kusan kashi tamanin cikin dari na kasuwancin nahiyar Afrika, tana yinsa ne da kasashen waje.
Haka kuma Alhaji Aliko Dangote yayi magana kan irin matsalolin da ‘yan kasuwan Afirka ke fuskanta a nahiyarsu wajen tafiye-tafiye. Yace idan shi da wani Ba’amarike sun nufi kasar Afirka ta Kudu hukumomin kasar zasu bar Ba’amariken ya shiga amma shi Dangote ba za’a barshi ba. Yace saboda haka ne suke matsawa a yi fasfo na nahiyar Afirka domin kowane dan kasuwan Afirka ya iya zuwa kowace kasa a nahiyar.
Shi ma tsohon shugaban Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo ya yaba da kafa kungiyar sai dai kuma yace akwai bukatar a jawo shugabannin hada-hadar kudi na nahiyar a hada kai dasu domin kungiyar ta samu nasara.
A nashi jawabin tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Thabo Mbeki ya aminta da cewa matsalar Afirka na tattare da rashin samun izinin zirga zirga cikin kasashen baki daya yayinda ‘yan kasuwa daga kasashen Turai da Amurka ke samun fifiko.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum