A halin da ake ciki kuma, fargabar da ta kunno kai a game da yiwuwar sa-in-sar cinikayya ta sa wadansu kasuwannin hannayen jarin Amurka da na kasashen Asiya faduwa jiya Laraba, biyo bayan murabus din mai ba shugaban Amurka shawarwari kan harkokin tattalin arziki.
Darektan majalisar harkokin tattalin arziki ta kasa, Gary Cohn, yana kan gaba wajen yin adawa da shirin shugaba Trump na kara kudin fito da kashi 25 kan Tama, da kuma kashi 10 cikin 100 a kan goran ruwa, ko farin karfe, da ake shigowa da su Amurka daga wasu kasashe.
A lokacin da yake jawabin bayyana murabus dinsa, Cohn ya ce “Na gode da damar da aka bani in bautawa kasata, na kuma gabatar da wadansu tsare tsaren da zasu amfani Amurkawa, musamman yin garambawul ga tsarin haraji na tarihi."
A hada-hadar da aka yi jiya a kasuwannin hannayen jari, alkaluman Dow Jones dake auna darajar masana'antu 30 mafiya girma a Amurka, sun fadi da kimanin kashi daya cikin 100 a lokacin bude kasuwa, amma daga bisani suka farfado, aka rufe kasuwa su na kasa da kimanin sulusin kashi daya. Alkaluman S&P sun fadi kasa kadan, a yayin da alkaluman kamfanonin fasaha na NASDAQ suka cira sama tare da muhimman alkaluman hannayen jari na kasashen Turai.
Tun farko a Asiya, alkaluman kasuwar hannayen jarin Hong Kong ta Hang Seng sun yi kasa da kashi 1 cikin 100, yayin da hannayen jarin Nikkei na kasar Japan suka fadi da kadan.