Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canada Taki Yarda Da Harajin Karafan Waje Da Amurka Ke Niyar Yi


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Firayi ministan kasar Canada Justin Trudeau yace ko kadan ba zasu amince da mataki da shugaban Amurka Donald Trump ke niyar dauka na dora harajin kashi 25 cikin dari a kan karafan da ake shigo dasu daga kasashen waje.

Trudeau yayi wadannan kalaman ne a jiya Juma’a, inda ya kara da cewar a shirye yake ya kare masana’antun Canada. Canada dai itace kasar waje da tafi samarwa Amurka wadannan karafan. Yayi kashedi cewa wannan harajin zai addabi Amurkawa masu amfani da wadannan karafan, saboda parashinsu zai haura.

Wannan mataki na Trump ya kuma shafi kungiyar Tarayyar Turai, inda shugaban hukumar zartarwar kungiyar Jean-Claude Junker, shima yayi kashedi cewa Tarayyara Turai zata rama wannan harajin daidai a kan kayan da ake yinsu a Amurka kamar barasan whisky da sutura da Babura.

Junker ya fadawa manema labarai jiya Juma’a a Jamus cewa, bai ji dadin Kalman da Trump yayi amfani dasu na Yakin Cinikayya ba.

Trump dai ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, Yakin cinikayya abu ne mai kyau kuma mai sauki wurin yin galaba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG