Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Kara Kudin Fito Akan Karafa Da Tama


Shugaban Amurka Donald Trump a tsakiya yayinda yake ganawa da shugabannin kamfanonin karafa da tama na Amurka inda ya fada zai kara kdin fito na karafa da tama da ake shigo dasu daga waje
Shugaban Amurka Donald Trump a tsakiya yayinda yake ganawa da shugabannin kamfanonin karafa da tama na Amurka inda ya fada zai kara kdin fito na karafa da tama da ake shigo dasu daga waje

Jiya shugaban Amurka Donald Trump ya cika alkawarin da ya yiwa jihohin da suke hako tama da karafa cewa zai kara kudin fito akan wadanda ake kawowa daga kasashen waje domin kare na gida

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada jiya Alhamis cewa Amurka zata aza kudin fito mai dan karen yawa a kan tama da karafa da ake shigowa da su daga waje.

Trump yace daga yanzu za a biya kudin fito na kashi 25 cikin 100 na kudin tama, da kuma kashi 10 cikin 100 na farashin karafan da za a shigo da su nan Amurka, sannan za a dauki lokaci mai tsawo ana aiwatar da wannan. Yace zai sanya hannu a kan wannan sabon matakin a wani lokaci cikin mako mai zuwa.

A sakon da ya aika daga shafinsa na Twitter a jiya alhamis, Trump yace, "An jima ainun ana durkusar da kamfanonin Tama da Karafa namu a saboda rashin tsarin ciniki na adalci da kasashe a fadin duniya." Ya ci gaba da cewa daga yanzu, ba zamu bari ana tauye hakkin kasarmu da kamfanoninmu da kuma ma'aikatanmu ba. Ya ce muna son ayi kasuwanci amma ayi shi bisa tsari, adalci da mutunci.

A wurin taron na jiya alhamis, Shugaba Trump yace Yarjejeniyar Cinikayya ta Kasashen Arewacin Amurka, NAFTA da kuma Kungiyar Cinikayya ta Duniya sun yi illa ga Amurka. Ya ce yunkurowar tattalin arzikin kasar China yazo dai-dai ne da lokacin da aka kafa hukumar cinikayyar ta duniya.

Trump ya shaidawa shugabannin kamfanonin Tama da Farar Karfe na Amurka cewa sauran kasashen duniya ba su yi ma Amurka adalci ba, amma kuma yace bai ga laifin kasashen ba.

Sai dai ba tare da sanin ko wasu kasashe ne kara yawan kudin fiton zai shafa ba, zai yi wuya a iya auna irin tasirin da wannan abu zai yi.

Musali a cikin shekarar 2017 kusan rabin Tamar da Amurka ta sayo daga waje ta fito ne daga kasashen Canada, Brazil, Koriya ta Kudu, da Mexico. Yawan Tamar da Amurka ta saya daga kasar China a shekarar ba ta kai ko da kashi 2 cikin 100 ba.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG