Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harajin Amurka: Za a Fafata a Fagen Kasuwannin Duniya Tsakanin Manyan Kasashe


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Ga dukkan alamu za a shiga gasa a kasuwannin duniya tsakanin manyan kasashe saboda martanin da kasar China ta ce za ta mayar muddun Amurka ta sa haraji kan karafa da dalmar kasashen waje.

Kasar China ta yi gargadin cewa za a fuskanci abin da ta kira ‘gagarimin sakamako’ a tsarin cinakayyar duniya, muddun Shugaban Amurka Donald Trump ya aiwatar da shirinsa na sa haraji da kashi 25% kan karafa, dalma kuma da kashi 10% matukar daga kasar waje aka kawo Amurka.

Wang Hejun, Shugaban Ma’aikatara Cinakayyar China ya fada a wani bayaninsa na daren jiya Jumma’a cewa labudda wannan harajin zai yi, abin da ya kira, “matukar illa ga tsare-tsaren kasuwanci da cinakayyar kasashe kamar yadda tsarin cinakayyar duniya na WTO ya tanada, kuma zai kawo rudami sosai ga yanayin cinakayyar duniya kamar yadda aka sani a yanzu.”

Jami’in na kasar China ya ce, “Idan wannan matakin na Amurka ya yi illa ga muradun China, kasar China za ta hada kai da sauran kasashen da abin ya shafa wajen mai da martani don kare ‘yancinsu da kuma muradunsu.”

A halin da ake ciki kuma, Firaministan Canada Justin Trudeu ya ce wannan shirin Trump na sa haraji ba a bin yadda ba ne.

Trudeau ya fadi jiya Jumma’a cewa a shirye ya ke ya kare masana’antun Canada.“ Kasar Canada ce ta fi shigo da dalma da karafa cikin Amurka.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG