Yakamata A Rage Wahalar Da Sojoji Yayin Horar Dasu-Inji Jami'ai A Nijer

Sojojin a Jamhuriyar Nijer

An yi jana’izar wani hafsan sojan da ya rasu a makarantar horar da jami’an tsaro dake kauyen Tondibiya cikin wani yanayi mai cike da hazo, lamarin da ya sa danginsa da jami’an fafutuka nuna bukatar bincike don gano masababin mutuwar wannan matashi.

An gudanar da addu’o’i a makarbartar unguwar Yantala bayan kammala jana’izar marigayi Tchombiano Talatou Chamsoudine hafsan sojan sama wanda Allah ya yiwa cikawa a wani lokacin da yake daukar horo domin kara gogewa a kan aiki a makarantar sojoji ta Tondibiya.

Rasuwar wannan matashi dan kimanin shekaru 22 a duniya, ta matukar sosa ran jama’a a birnin Yamai. Alh. Nouhou Arzika na cikin ‘yan rajin kare hakkin dan adam din da suka halarci wannan taron jana’iza.

Wannan ya sa dangin marigayi Tchombiano Talatou Chamsoudine nuna bukatar a gudanar da bincike don gano zahirin dalilan mutuwar dan uwansu.

Su ma dai jami’an fafutuka na ganin lokaci ya yi da ya kamata a dauki matakan kawo karshen duk wasu ayyuka da suka sabawa ka’ida a yayin horar da jami’an tsaro.

Tuni dai aka dakatar da jami’an soja da likitan da ke kan aiki a lokacin da wannan al’amari ya faru a matsayin wani matakin share fagen bincike, inji ministan tsaron kasa Kalla Moutari wanda yace gwamnati na da niyar biyawa iyayen mamacin dukkan wata diyyar da doka ta yi tanadi..

Rasuwar Tchombiano Talatou wacce ainihi ta fara bayyana a shafin facebook a ranar 8 ga watan nan na Disamba, ta haddasa babbar mahawara a tsakanin jama’a wadanda galibinsu ke nuna shakku a game da ainihin ajalin wannan yaro wanda gawarsa ke dauke da manyan raunika.

Ga rahoton Sule Mumuni Barma daga birnin Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

AN CE A RAGE WAHALAR DA SOJOJI YAYIN HORO