Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar IFAD Za Ta Farfado Da Harkar Noma a Zimbabwe


Hukumar asusun raya noma ta kasa da kasa ta Majalisar Dinkin Duniya IFAD a takaice ta shirya zuba jari a Zimbabwe a karon farko tun bayan shekaru da dama.

Hukumar IFAD ta kai ziyara a Zimbabwe kuma ta kyautata zaton zata farfado da sashen nomar kasar bayan shekaru da dama ta taki yin haka.

A shekarar 1999 asusun raya noma na kasa da kasar ya tallafawa fara wani aikin nomar rani mai girmar kimanin kilomita 120 a gabashin birnin Harare.

Al’ummar yakin sun ce wannan aiki ya taimakawa rayuwarsu wurin samar da abinci da kudin shige da kuma aikin yi.

Hukumar IFAD tace ta ware sama da dala miliyan 41 domin taimakawa nomar rani tsakanin shekaru uku, a wannan lokaci da aka samun daidaituwar al’amura a nan Harare.

Shugaban IFAD Gilbert Houngbo ya ce idan aka dakatar da wata kasa a cikin wannan shiri ko Zimbabwe ne ko kuma wata kasa dabam abin damuwa ne, amma kuma ya ce yakamata kusan cewa muna da kudin da zamu yi aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG