A shekarar 1948 ne kasashen duniya suka rattaba hannu akan wata yarjejeniyar amincewa muhimman hakkokin dan Adam bayan lura da ukubar da jagoran Jamusawan wancan lokoci Hitler ya ganawa abokan gabarsa a zamanin yakin duniya na biyu, saboda haka ranar ta 10 ga watan Disamba ke zama wani lokaci na bitar halin da ake ciki a fannin ‘yancin dan Adam.
Sai dai shekaru 70 bayan wannan alwashi har yanzu ana fuskantar jan kafa a wannan fanni a nafiyar Afirka, inji magatakardar hukumar kare dan Adam ta CNDH mai shari’a Amadou Alichina kourgeni.
Matsalar tsaron da aka shiga a kasashen dake fama da hare haren ta’addanci a yau, na daga cikin matsalolin da suka hanawa jama’a morar ‘yanci da dama.
Binciken hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH a wasu yankunan karkara ya yi nuni da cewa ana ci da hakkin makiyaya a wurare da dama a Nijar.
Garkame ‘yan kasa ba tare da wata kwakwarar hujja ba wani bakon al’amari ne da kungiyoyin fafutika suka ce yana neman samun gindin zama a wannan kasa saboda haka suka lashi takobin yakar wannan dabi’a dai dai da abin da doka ta yi tanadi.
Shagulgulan ranar ta bana sun tahallaka ne wajen kiraye-kirayen al’umomin duniya akan bukatar su tashi tsaye don kwatar ‘yanci wato Stand Up For Your Rights.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum