A yau Litinin, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gueterres, ya bayyanar da cewar ya kamata "Batun hijira ya kasance cikin tsari, kuma mara hadari." Yayin da yake yaba ma tawagar da ta kunshi kasashe sama da 150, wadanda su ka taru don cimma wata yarjajjeniyar kasa da kasa, da zummar inganta yadda duniya ke daukar batun kaurar jama'a.
A jawabin da Guterres ya yi a birnin Marakesh na kasar Morocco, ya jinjina ma kasashen da ke da tasiri kan batun -- wadanda akasari kasashen Nahiyar Turai ne.
Wadanda ke da muhimmanci sosai kan batun tsara kaurar jama'a a matakin kasa da kasa, cikin natsuwa da rashin hadari ga jama'a.
Ya ce wadanda ke fargabar cewa yarjejeniyar na iya saba ma diyaucin kasa, ta wajen tilasta amfani da wasu tsare-tsare na kaurar jama'a, ko kuma tasa ya zama tamkar 'yanci ga duk mai son kaura zuwa duk inda ya ke so, kana a duk lokacin da ya ga dama, to ba su fahimci abin ba ne.
Facebook Forum