Yadda 'Yan Najeriya Suka Yi Zanga-Zanga A London Don Neman Gwamnati Ta Samar Da Tsaro A Arewa

#securenorth

Kungiyar daliban arewa masu karatun digiri na daya zuwa na uku a kasar Burtaniyya sun gudanar da zanga-zangar lumana don mika kokensu a game da yanayin tabarbarewan tsaro a arewacin kasar.

A wani mataki na ci gaba da yin kiraye-kirayen gwamnatin tarayyar Najeriya ta samar da tsaro a yankinsu, wanda suka yi wa take da #Securenorth, kungiyar daliban arewa masu karatun digiri na daya zuwa na uku a kasar Burtaniyya sun gudanar da zanga-zangar lumana don mika kokensu a game da yanayin tabarbarewan tsaro a arewacin kasar.

#securenorth

Kiraye-kirayen neman gwamnati ta sauke nauyin da ya rataya a yuwanta na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin kasar da aka yiwa take da secure north a turance musamman na baya-bayan nan ya kara kamari ne a kafafen sada zumunta baya ga kona matafiya sama da 40 da yan bindiga suka yi a jihar Sokoto da sauran kashe-kashe a yankin arewa maso yamma da tsakiya.

A dandalin Trafalgar dake kasar Ingila dalibai da mazauna birnin London da kewaye 'yan asalin arewacin Najeriya sun fito zanga-zangar lumana don farkar da gwamnatin Najeriya da shugaba Buhari ke jagoranta ta yi amfani da sauran lokacin da ya rage mata kan karagar mulki wajen fitar da yankin arewa daga kangin matsalolin tsaro da talauci da suka yiwa yankin katutu.

Dalibai mata da maza da wasu mazauna kasar ingila dai sun ce tura ta kai bango a kan matsalolin tsaro da ke ci gaba da tsananta a arewacin Kasar, lamarin da mai magana da yawun shugaba Buhari, mallam Garba Shehu ke ci gaba da cewa, gwamnati na daukan matakan da suka dace.

Su kuwa ana su bangaren mutanen kasarna ganin gwamnatin bata nuna damuwa yadda ya kamata ta duba da yadda rayuka ke salwanta a ko wace rana ta Allah a kasar.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yadda 'Yan Najeriya Suka Yi Zanga-Zanga A London Don Neman Gwamnati Ta Samar Da Tsaro A Arewa