Wasu daga cikin gungun ‘yan mata daliban makarantar sakandaren da ‘yan ta’adda suka kaiwa hari a jihar Bornon Nigeria, sun yi bayanin yadda suka yi sa’ar kubuta daga kangin daga ‘yan Boko haram suka yi wajen shirya kamesu a gidajen kwanansu na makaranta.
WASHINGTON, DC —
Dalibar wadda muka boye sunanta tace "yayin da aka kaimu wani daji sai su ‘yan matan suka fara tunanin cewa tun da wasu daga cikin ‘yan matan da aka kama sun yi tsalle daga cikin motar domin kubuta kuma Allah Ya basu sa’ar kubutar, mai zai hana muma mu jarraba yin tsallen domin mu kubuta koda kuwa ‘yan ta’addar zasu kashemu a lokacin? Domin yanzu dai bamu san inda ‘yan bangar zasu kaimu ba, don haka sai ini da kawata muka tari aradu daka muma yi tsalle daga cikin motar suka tsere da gudu."
Kutsawa da ‘yan banga suka yi har suka sace dalibai ‘yan mata hakan yaketa haddin mutumcin Bil Adama don haka ya zama wajibi kan kasa da kasa da suyi wani abu.
Amurka na daga cikin kasashen da yanzu haka ke bada gudummawar bincike da kayan aiki, sauran kasashen dake aiki kan haka sun hada da Birtaniya, kuma hukumomin Nigeria sun yi alkawarin bada Tukuicin Dolar Amurka dubu dari uku ga duk wanda ya basu cikakken labarin da zai taimaka masu sanin wurin da aka kai daliban aka boye.
Ya zuwa yanzu dai babu bayanai akan makomar ragowar daliban mata su kusa 300.