A yayin da al'umar Musulmi ke murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi-Wasallam, wasu mahalarta taron Mauludin na bana a jihar Kaduna sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su.
Al'umar garin Kwandari da ke karamar hukumar Lere a jihar Kaduna, suna kan hanyarsu ta zuwa wajen taron Mauludin na bana ne wani mai babbar mota ya afka musu a kokarin kaucewa mai babur.
Rukunin mutanen garin Kwandari da ke karamar hukumar Lere a jihar Kaduna da suka haura 60 ne dai suka cika wata babbar mota don zuwa taron Mauludin da akan hanya ne kuma wannan iftila'i ya auku.
Wasu al-umar garin Kwandarin dai sun ce akalla mutum arba'in sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama su ka jikkata.
Daya daga cikin 'yan uwan wadanda suka rasu ya ce kokarin kaucewa mai babur a kan kwana ne ya sa babbar motar ta afkawa motar da ke dauke da masu Mauludin inda nan take sama da mutane ashirin su ka riga mu gidan gaskiya.
Nan kuwa a garin Kaduna taron Mauludin ya tashi lafiya ba asarar rai kuma ya sami halartar dubban mutane ciki har da babban malamin addinin Kiristan nan, Pastor Yohanna Buru kuma ya ce wajibi ne al-umar Najeriya su dunkule waje guda don tunkarar matsalolin dake damun kasar.
Malaman addinin musulunci da dama ne su ka yi jawabai, kuma wasu daga cikin su sun ce hadin kan al-umar Najeriya a wannan lokaci ya zama wajibi saboda matsalolin kasar sun shafi kowa.
Dama dai duk shekara a irin wannan wata na Rabiyu-Awwal, al-umar musulmi ke murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammadu ta hanyar tarurrukan tarihin fiyayyen halittan da kuma shan shagulgula kuma a irin wannan lokaci ne bara wasu masu Mauludin su ka riga mu gidan gaskiya sakamakon jefa musu bom cikin dare.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:
Your browser doesn’t support HTML5