Gwamnatin Jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriay ta cire dokar hana fita a yankin garin Kaduna da Zaria.
Wata sanarwa da kwamishinan cikin gida da tsaro Samuel Aruwa ya fitar a ranar Talata, ta ce an janye dokar ne bayan nazari da aka yi kan kyautatuwar al’amuran da suka shafi tsaro a jihar.
“Matakin cire wannan doka ya fara aiki nan take – daga yau Talata 13 ga watan Agustan 2024.
“A dalilin haka, ana umartar jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin walwala a Kaduna da Zaria.” Aruwan ya ce.
A daren Litinin majalisar tsaron jihar ta Kaduna ta yi wani zama inda mambobinta suka amince da a cire dokar ta hana fita wacce aka saka sanadiyyar barkewar tarzoma a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a wasu sassan Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna