WASHINGTON, D. C. - A cikin kwanaki masu zuwa, ta yi ƙoƙari ta bi masu garkuwa da mutanen har cikin dajin, amma 'yan uwanta suka sanar da sojoji wadanda suka kamata suka dawo da ita gida.
A karshe dai ta sayar da kayanta kadan da suka hada da tukwane, fanka da talabijin, sannan ta nemi taimakon ‘yan uwanta da surukanta, da kuma ‘yan cocin yankin, domin ta biya kudin fansa na Naira miliyan biyu a lokacin dalar Amurka $1,256, don ta tabbatar da sakin ‘yarta.
Precious, wanda aka yi garkuwa da ita daga makarantar sakandaren Bethel Baptist ta Maraban Damish a jihar Kaduna, ta dawo gida bayan wata daya da aka yi garkuwa da ita, kamar yadda mahaifiyarta Esther ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Kungiyar Boko Haram dai, mai da’awar jihadi ta fara aiwatar da sace-sacen mutane a makarantu a Najeriya, wadda ita ce kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka, inda ta kwace dalibai 276 a makarantar ‘yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno shekaru goma da suka gabata. Wasu daga cikin ‘yan matan dai har yanzu ba a sake su ba.
Sai dai tun daga lokacin ne kungiyoyin masu aikata laifuka suka rungumi wannan dabarar ba tare da wata alaka da akidar neman kudin fansa ba, inda da alama hukumomi ba su da ikon hana su.
Yayin da tattalin arzikin Najeriya da talauci ke kara tabarbarewa, satar mutane ya zama ruwan dare kusan kullum a 'yan shekarun nan, da kuma neman kudin fansa a kansu.
A ranar 7 ga Maris ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai 286 wasu ‘yan kasa da shekaru takwas da kuma ma’aikatan makarantar a garin Kuriga da ke jihar Kaduna. Hukumomin yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba cewa masu garkuwan sun bukaci a biya su jimillar Naira biliyan 1, kwatankwacin sama da dala 620,000 domin a sako su.
A kuma daren ranar Litinin, aka sace mutane kusan 60 a Buda, dake cikin jihar ta Kaduna, mazauna yankin sun ce wanda ya kawo adadin wadanda aka yi garkuwa da su a fadin kasar cikin makonni biyu na farkon watan Maris zuwa kusan 750, a cewar Amnesty International.
"Sace mutane don neman kudin fansa ya wuce sauran dalilai na sace-sacen mutane, musamman dalilai na siyasa," in ji kamfanin bincike na SBM Intelligence a cikin rahoton na Yuli 2023.
Da yake magana game da garkuwa da dimbin mutane da aka yi a garin Kuriga a makon jiya, Ministan yada labarai Mohammed Idris a ranar LAraba ya bayyana cewa matsayin gwamnati shi ne jami’an tsaro su tabbatar da sako mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan ko sisin kwabo ba domin neman kudin fansa. Biyan kudin fansa ga wadanda suka yi garkuwa da mutane laifi ne a Najeriya tun shekarar 2022 da kuma hukuncin daurin akalla shekaru 15 a gidan yari.
To amma satar mutane dai na tarwatsa iyalai da al’ummomin da sai sun hada kudaden da suka tara domin biyan kudin fansa, lamarin da ke tilasta wa iyaye sayar da dukiyoyin da suka fi daraja kamar filaye da shanu da hatsi domin a sako ‘ya’yansu.
Yayin da Precious ta koma makaranta kuma a yanzu tana karatun alakar kasa da kasa a shekarar farko ta jami'a, wasu da dama da aka sace sun bar karatu kwata-kwata bayan an sako su, saboda fargabar sake sace su.
Akalla yara miliyan 10.5 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya, adadi mafi yawa a duniya, a cewar hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF. Hakan na faruwa ne sakamakon rashin tsaro da suka hada da sace mutane da kuma tada kayar baya da aka dade ana yi a yankin arewa maso gabas.
Sace-sacen mutane “babban abin da ke jawo janye yara daga makarantu a arewacin Najeriya ne,” in ji Isa Sanusi, darektan Amnesty International a Najeriya.
“Babu iyayen da ke son shiga cikin firgicin da wasu ‘yan bindiga marasa tausayi suke jefa su bayan sace ‘ya’yansu. A kai, a koma, ana rufe makarantu saboda matsalar tsaro, sannan yaran suna rasa ilimi, saboda yawanci ana yi wa ‘yan mata fyade idan an sace su, ‘yan matan da yawa ana cire su daga makaranta kuma ana yi musu aure tun suna kanana."
-Reuters