Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Dauki Alhakin Sace 'Yan Makarantar Katsina


Kungiyar mayakan Boko Haram.
Kungiyar mayakan Boko Haram.

A jiya Talata, ‘yan tawaye daga kungiyar ta’addancin Boko Haram sun dauki alhakin sace daruruwan yaran maza daga wata makaranta a jihar Katsina dake arewacin Najeriya a makon da ya gabata a wani gagarumin hari a wannan shekara, lamarin da haifar da fargaba da bazuwar tashin hankali a yankin.

Sama da dalibai 330 ne ba a gano su ba daga makarantar sakandaren gwamnatin ta koyar da kimiya a garin Kankara, bayan da ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a makarantar a ranar Juma’a, koda yake wasu daliban sun samu sun arce.

Gwamnati da maharan suna tattaunawa a kan makomar yaran, a cewar Mallam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Ya ce “maharan sun yi tuntuba kana ana nan ana tattaunawa dasu a kan batun kare lafiyar yaran da kuma dawo dasu gida, inji Mallam Shehu a wani sakon Twitter yayin da yake magana gwamnan Katsina Aminu Masari.

Sai dai jami’in bai bayyana ko da Boko Haram ake tattaunawar ko kuma wata kungiya daban.

Gwamna Masari ya ce hukumomin tsaro dake aikin ceto yaran sun fada cewa sun gano inda ake tsare da yara.

A jiya Talata, Amurka ta yi Allah wadai da kakkausar murya game da sace yaran makaranta sama da 300 daga makarantar su a arewa maso yammacin Najeriya kana tana bincike a kan ikirarin Boko Haram na daukar alhakin kai harin, inji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

A wani sakon faifan sauti a kan harin na ranar Juma’a, Shekau ya ce kungiyar sa ce ta sace yaran makarantar saboda koyarwar kasashen yammacin duniya da ake yi a makarantar sun sabawa koyar addinin Musulunci.

Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, da jihar Katsina.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG