Yadda Birnin Dubai Zai Ci Moriyar Gasar Cin Kofin Duniya Da Za A Yi A Qatar

Kasar Qatar

Tuni dai kamfanonin jiragen sama, wuraren shakatawa, gidajen sayar da abinci da kantunan kayan alatu suka fara wasa wukakensu don tarbar baki.

Yayin da ake shirin fara karawa a gasar cin kofin duniya a Qatar a watan Nuwamba mai kamawa, Dubai da ke kasar Hadaddiyar Daular Laraba na shirin karbar dubban baki saboda kusancin birnin da kasar ta Qatar.

Tafiyar minti 45 ne a jirgin sama daga Dubai zuwa Qatar, wacce ke shirin karbar masoya kwallon kafa akalla miliyan 1.2.

Sai dai masana sha’anin tattalin arziki sun yi kiyasin cewa, da yawa daga cikin wadanda za su je kallon gasar, za su yada zango a Dubai, saboda kusancin birnin da Qatar.

Tuni dai kamfanonin jiragen sama, wuraren shakatawa, gidajen sayar da abinci da kantunan kayan alatu suka fara wasa wukakensu don tarbar baki.

Cikin shekaru 20 da suka gabata, Dubai ta ga bunkasa a fannin yawon bude ido lamarin da ya sa mutane daga sassan duniya suke tururuwar zuwa birnin.

Ko da yake, fannin yawon bude idon birnin ya tagayyara a baya-bayan nan sanadiyyar barkewar annobar COVID-19, amma ana ganin wannan gasa ta cin kofin duniya za ta sa ya samu cikakkiyar farfadowa.

Za a fara gasar daga ranar 21 ga wata Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar bana.