Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino ya ce a shekarar 2022 kasashe 48 ne za su halarci gasar cin kofin duniya, wacce za a yi a kasar Qatar dake daular larabawa.
A da dai an shirya fara amfani da tsarin kasashe 48 ne a shekarar 2026, inda kasashen Amurka, Canada da kuma Mexico za su karbi bakuncin gasar.
Kasashe 32 ne suke halartar gasar ta cin kofin duniya inda a bana aka yi a kasar Rasha wace kasar Faransa ta lashe wasan.
Wannan sauyin zai tilasta wa Qatar ta nema hadin gwiwa da wasu kasashe a yankin Gabas ta Tsakiya, don karbar bakuncin gasar, a cewar shugaban hukumar ta FIFA.
Muna duba yiwuwar hakan, muna tattaunawa da abokanmu a Qatar da sauran kawayenmu da ke yankin, kuma muna fatan hakan mai yiwuwa ne.
Shugaban na FIFA Gianni Infantino, yayi wannan bayanin ne a lokacin da yake jawabi a babban taron hukumar kwallo kafa ta Nahiyar Asiya, a sabuwar shelkwatar hukumar dake Birnin Kuala Lumpur a kasar Malaysia.
Inda ya kara da cewar, ya kamata abai wa kowace kasa damar
fafatawa a gasar cin kofin duniya.
Facebook Forum