Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya 2018


Mo Salah A Kan Benci
Mo Salah A Kan Benci

Misra tasha kashi a hannun Uruguay da ci daya ba ko daya a yau.

A jiya Alhamis ne aka fara buga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya inda mai masaukin baki wato Rasha ta lallasa kasar Saudi Arabiya da ci biyar babu ko daya a wasan farko na bude gasar.

A yau juma’a ne kasar Misra ta kara da ta Uruguay inda kasar Uruguay tayi nasarar saka kwallo daya a zare, a yayin da Morocco zata kafsa da Iran sai kasar Portugal da zata warwasa da Spain.

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya halarci bikin bude gasar wanda akayi shi a filin kwallo na Luzhniki mai mazaunin yan kallo dubu 80 a Moscow.

Rasha dai ta kashe kimanin dalar Amurka biliyan 13 domin daukar nauyin wasannin da za’ayi a birane 11.

Daga cikin manyan kasashen da suka shahara a kwallon kafa da ba’a gani ba a wannan gasar sun hada da kasashen Italiya da na Netherlands

Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta bayyana cewar kimanin mutane biliyan uku ne suka kalli wani bangare na wasan gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da aka gabatar a baya, yayin da wasu biliyan guda suka kunna talabijin dinsu domin kallon wasan karshe da aka fafata tsakanin Jamus da Argentina.

Kasar Qatar itace wacce zata zamo mai masaukin baki na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za’ai tsakanin watannin Nuwamba da Disamba na shekarar 2022 sai kuma hadakar kasashen Amurka da Mexico da Canada da zasu karbi gasar a shekarar 2026.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG