A jiya Litini ne Hukumar Hana Amfani Da Shan Abin Kara Kuzari ta Duniya wato da turanci World Anti-Doping Agency ta hana kasar Rasha shiga ko wane irin wasaa duniya har sai bayan shekaru 4. Wasannin sun hada da 2020 Tokyo Olympics, da na cin Kofin Duniya wato 2022 World Cup da za a yi a kasar Qatar. Wannan dokar hana shiga wasannin Duniya, ta biyo ne bayan tuhumar ‘yan Rashar da amfani da kwayoyin kara kuzarin 'yan wasa.
Wannan matsi na dokar, har ya shafi manyan jami’ai na kasar ta Rasha, domin kuwa su ma an hana su zuwa ko wane taron wasanni na musamman.
Rahoto ya yi nuni da cewa an bai wa Rasha wa’adin daidaita al’amuranta da na 'yan wasanta, amma ba ta yi haka ba, dalilin da yasa kenan aka hana su shiga wasannin Duniya na Olympics.
Karin rahoto ya ce ‘yan Rasha na da izinin ta shiga wasannin kwallon kafa na Duniya a 2022, amma har idan su ka zama zakarun wasan kwallaon kafar, ba za a ba su izinin zuwa kammala gasar a Qatar ba.
Firaministan Rasha Dmitry Medvedev, ya ce duk wannan ba wani abu ba ne illa siyasar duniya da duniya ke yi ma kasarsa.
Ga masu gani da sauraro, mene ra'ayinku game da shaye shayen miyagun kwayoyi da 'yan wasa ke yi domin kara zuzari ko samun nasara?
Facebook Forum