Ma’aikatan majalisun tarayyar Amurka da jami’an fadar White House sun gana a jiya Asabar a nan Washington, a wani kokarin kawo karshen rufe wani bangaren gwamnati da ya shiga kwana na cikon 15, kuma an kammala wannan tattaunawa bayan wasu sa’o’i. Bangarorin biyu na kuma shirin ganawa a yau Lahadi.
WASHINGTON DC —
Cijewa da aka samu a kan bukatar shugaba Donald Trump na dala biliyan biyar da miliyan dari shida domin gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico ne ya yi sanadiyar rufe gwamnatin.
Mataimakin shugaban kasa Mike Pence, da ya gana da shugabannin majalisun biyu ya kwatanta tattaunawar a wani sakon Twitter da mai ma’ana, sai dai an kammala tattaunawar ba tare da cimma matsaya ba.
Jim kadan shima shugaba Trump ya aike da wani sakon Twitter yana mai cewa ba a samu wata fahimtar juna ba a yau.
Ita kuwa kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ta fitar da wata sanarwa a jiya Asabar, inda take cewa wannan matakin rashin hankali da damuwa da Trump ya dauka na rufe gwamnati, yakamata ya zo karshe.