Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea Ta Arewa Ta Kalubalanci Amurka Kan Alkawarin Da Ta Yi


Shugaba Kim Jong Un a wani hoton bidiyo da ba ambaci ranar da aka dauka ba, yana jawabi
Shugaba Kim Jong Un a wani hoton bidiyo da ba ambaci ranar da aka dauka ba, yana jawabi

“Amma idan Amurka ta kai mu makura, har ta tilasta wani abu akanmu, ta hanyar kakaba takunkumi ba tare da cika alkawuran da ta dauka a gaban duniya ba, ba mu da wani zabi, da ya wuce mu dauki wata sabuwar hanya.” In ji shugaba Ki

Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jon Un, ya yi gargadin cewa, zai kawo karshen ‘yar fahimtar da aka samu tsakanin kasarsa da Amurka, muddin Amurkan ba ta daina ci gaba da yunkurin ganin an kakaba takunkumin da zai tilasta mata kwance damarar makaman nukiliyanta ba.

Yayin jawabin murnar sabuwar shekara da ya saba yi, Kim, ya ce Korea ta Arewa ta kuduri aniyar kin ci gaba da samar da makaman na nukiliya ko kuma yin gwajinsu.

“Amma idan Amurka ta kai mu makura, har ta tilasta wani abu akanmu, ta hanyar kakaba takunkumi ba tare da cika alkawuran da ta dauka a gaban duniya ba, ba mu da wani zabi, da ya wuce mu dauki wata sabuwar hanya, wacce za ta kare ‘yan cin kasarmu tare da samar da zaman lafiya a yankin tekun Korea.” In ji shugaba Kim.

A lokacin wani taron koli da suka yi a bara a kasar Singapore mai cike da tarihi, Shugaba Trump da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, sun cimma wata kwaryakwaryar matsaya a watan Yuni.

Amma an gaza dabbaka matsayar, saboda wasu dumbin bukatun da Korea ta Arewa ta nema, na sassauta mata takunkunmin da aka saka mata, da kuma adawar da ta nuna kan bukatar da hukumomin Washington suka mika, ta neman Korea ta Arewan ta kwance damarar makamanta, kafin a dage mata takunkman.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG