Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kai Ruwa Rana A Kan Batun Rufe Gwamnatin Amurka


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Da alamar batun rufe wani bangaren gwamnatin Amurka ba zai kare nan da nan ba, yayin da hadiman fadar White House da na majalisun tarayya zasu yi ganawa a karshen mako.

Anasa ran ganawar ta karshen mako zata shawo kan matsalar da taki ci taki cinyewa na gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico da shugaban na Amurka Donald Trump ke niyar yi.

Trump ya fada a jiya Juma’a cewa an yi tattanawa mai ma’ana a ganawar da ya yi da shugabannin majalisun tarayya a kan warware batun rufe gwamnati biyo bayan rashin fahimta da aka samu a kan dala biliyan biyar da dubu dari shida na gina katangar.

Amma shugabannin majalisun na bangaren Democrats sun fadi akasin haka a kan ganawa da suka yi da fadar White House.

Kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ta Democrat, da aka rantsar da ita a shekaranjiya Alhamisa a shugabancin majalisar, ta kira ganawar ta sa’o’I biyu da mai cike da takaddama. Ta ci gaba da batun da nace akai cewa sai an bude gwamnati kana a warware batun kudin gina katangar.

Shima Chuck Schummer shugaba a majalisar dattawa ya fadawa manema labarai cewa, shugaban kasa ya yi barazanar rufe gwamnati tun da dadewa wurin watanni ko kuma shekaru.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG