Makon jiya ne dai kungiyar Transparency International, kungiyar dake yaki da cin hanci da rashawa, ta ce nasarorin da Najeriya ta samu can baya a kan yaki da cin hanci da rashawa sun ragu, kasar tana komawa baya zuwa gidan jiya.
Amma wata kungiya ta maida martani akan lamarin tare da bayyana bukatar matasa su tashi haikan akan yadda za'a kawar da cin hanci da rashawa a tsakanin al'ummar kasar
Dalili ke nan wata kungiya mai suna New Nigerian Nationalist ta 'yan kishin kasa ta bayyana cewa akwai bukatar matasa su tashi su tabbatar an kwato kasar daga abun da ta kira tabarbarewa ko ma rugujewar kasa baki daya.
Paul Irene shugaban kwamitin amintattun kungiyar ya ce akwai bukatar shugaba Muhammad Buhari ya ja damara tare da goyon bayan al'ummar kasar na ganin an kawar da cin hanci da rashawa. Ya kara da cewa su matasa zasu tashi su tunkari lamarin su nuna basa so.
Kungiyar New Nigerian Nationalist da wasu daga cikin 'ya'yanta sun fara wani tattaki daga birnin Lagos zuwa Abuja tun watan Janairu domin fadakar da al'umma da gwamnati akan bukatar tashi tsaye a kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar.
Hajiya Sa'adatu Ali Shuwa ta ce sun fito ne a kungiyance domin su nuna wa jama'a cewa Najeriya ta na cikin wani halin kunci. Shugaba Muhammad Buhari shi kadai ba zai iya yakin ba sai duk 'yan kasar sun tashi su taimaka masa. Injita dalili ke nan da suka fito domin su taimakawa gwamnati yaki da mugun halin da ake ciki.
A saurari rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5