Nan bada jimawa ba, gwamnatin jihar Jigawa zata farfado da tsarin biyan kudaden akwati na wata-wata ga al’umomin kauyuka da garuruwa wanda tsohon gwamnan Jihar Sanata Saminu Turaki ya bullo dashi fiye da shekaru 10 baya.
Yanzu haka dai majalisar dokokin jihar zata yi doka akan haka, amma wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari, ya ambaci masana shari’a na cewa, dokar ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Karkashin wannan tsari na biyan kudin akwati, gwamnatin jihar ta wancan lokaci bisa jagorancin gwamna SaminuTuraki tana kebe wani adadin kudi a duk karshen watan domin raba su ga jama’ar garuruwa da kauyuka bisa tsarin akwatunan zabe da yawan su ya kai kimanin dubu 4 a fadin jihar.
Duk da shan sukar da tsarin yayi tun a wancan lokaci, fiye da shekaru 10 bayan shudewar gwamnatin Sanata Turaki, gwamnatin Jigawa ta yanzu bisa jagorancin gwamna Badaru Abubakar ta yunkura wajen farfado da tsarin, amma ta sigar bayar da kariyar shari’a, inda har ma ta shirya kudirin doka kuma aka mikawa majalisar dokokin jihar domin ya zama doka.
Shugaban kwamitin kula da harkokin shari’a da dokoki na majalisar dokoki ta jihar Jigawa, Bala Hamza Gada, yace bisa tsarin dokar da za a kafa, gwamnatin jiha da kuma kananan hukumomin da abin ya shafa zasu gutsuro wani abu wanda za a ba kwamitin kowace al'umma inda akwai akwatin zabe.
Yace 'yan kwamitin sune zasu zauna su yi shawarar irin aikin da za a yi da wannan kudin ma al'ummarsu.
Tuni dai masu nazarin doka da shari’a a Najeriya ke cewa, samar da wannan doka cin iyaka ne ga hurumin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba iwa kananan hukumomi.
Barrister Malam Abdullahi wani lauya mai zaman kansa, yace duk wani abinbda ya shafi aikin raya karkara ko al'umma, tsarin mulki a fili ya dora nauyinsa a kan kananan hukumomi ne.
Yanzu haka dai Jam’iyyar PDP tace zata dauki matakin shari’a game da wannan batu. Alhaji Aminu Jahun, mataimaki shugaban Jam’iyyar a jihar Jigawa, yace 'yan majalisar su na son su halalta ma kawunansu kudaden jama'a ne wadanda ba nasu ba.
Facebook Forum