A firarta da kakakin hukumar kwastan John Attah, Muryar Amurka ta ce akwai korafe korafe da yawa akan yadda hukumar take kwace kaya da motoci daga mutane.
John Attah dake magana da yawun hukumar kwastan ya ce ba kwace suke yi ba kamawa su keyi. Yace doka ta basu izinin kama duk kayan da aka shigo dasu ba kan ka'ida ba. Da zara sun sabawa dokar kasa za'a kamasu. Misali doka ta hana shigo da shinkafa ta kan iyakoki amma ta yadda a shigo da ita ta jiragen ruwa. Ma'ana, shinkafar da aka shigo da ita ta kan iyaka idan an kama ta zama kayan gwamnati kuma wanda ya shigo da ita zai fuskanci hukumci.
Idan mutum ya shigo da kaya kan ka'aida amma kuma ya ki biyan haraji dole ne su kama kayan har a biya ko kuma ya zama na gwamnati. Haka ma duk motar da aka shigo da ita ta kan iyaka idan an kama ta zama ta gwamnati. Amma idan ya shigo da ita ta tashar jirgin ruwa haraji kawai zai biya.
Akan motocin da hukumar ta tara a wasu garuruwan kasar, John ya ce sun fara yin gwanjo motocin ta yanar gizo kamar yadda doka ta basu izinin yi. Kawo yanzu mutane fiye da 7000 sun saye motocin dake Ibadan, Sokoto, Katsina da Lagos. Akan yin anfani da yanar gizo John Attah ya ce domin gujewa yin cuwa-cuwa ya sa suke anfani da yanar gizo.
Ga cikakken firar da Medina Dauda ta yi da John Attah na Hukumar Kwastan
Facebook Forum