A wajen wani babban taron shekara-shekara na fastocin majami’ar Ekilisiyar 'Yan uwa ta Najeriya,EYN, da aka gudanar a shedikwatar majami’ar ta Najeriya a Kwarhi,shugaban cocin Ekilisiyar,Rabaran Joel Billi,yace yanzu haka al’ummomin da suka koma yankunan a kananan hukumomin Madagali,Chibok,da Gwoza na cikin yanayin zaman dar-dar sakamakon harin sari-ka,noke da garkuwa da mata da kananan yaran da mayakan Boko Haram keyi a wadannan yankuna.
Ya ce kamata yayi gwamnatin Najeriya ta dau mataki kan shawo kan wannan matsala da sake gina garuruwan da aka lalata ta yadda jama’a zasu samu natsuwa.
Haka nan kuma ,shugaban majami’ar ya bukaci gwamnatin jihar Adamawa data sake gina musu majami’un da masallatan da 'yan Boko Haram suka lalata musu a jihar ,kamar yadda gwamnatin jihar Borno ta yi.
Kimanin dai fastocin cocin 112 ne suka sami halartar taron na kasa baki daya,inda a karshe aka yiwa Najeriya addu’a ta musamman
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum