WASHINGTON, D. C. - 'Yan kungiyar ‘Sexual Minorities Uganda (SMUG)’ sun fara shigar da karar ne a babbar kotun kasar a shekarar 2015 bayan da magatakardar kamfanoni na gwamnati ya ki amincewa da buga sunan kungiyar, wanda zai ba ta damar gudanar da ayyukanta bisa ka'ida, tana mai cewa wannan sunan "da ba a so ne".
Har ila yau, ta ce a lokacin kungiyar ta nema inganta muradun mutanen da dokokin Uganda ta haramta. A shekarar 2022, gwamnatin Uganda ta dakatar da ayyukan SMUG saboda ba a yi masa rajista a hukumance ba.
Dangantakar jinsi daya ta kasance haramtaciya a Uganda tun lokacin mulkin mallaka na Burtaniya kuma kasar ta kafa daya daga cikin dokokin yaki da LGBT mafi tsanani a duniya a watan Mayu, wanda ya haramta "inganta" luwadi.
Shari’ar da aka yanke ranar Talata, daukaka ce ta hukuncin wata karamar kotu daga shekarar 2018 da ta yanke hukunci kan kungiyar SMUG, daya daga cikin fitattun kungiyoyin kare hakkin LGBT a Uganda.
"Kotun ta yanke hukuncin cewa tun da manufar kungiyar SMUG shine inganta haƙƙin mutanen da dokokin Uganda ya haramta wa aiwatar da ayyukansu, to mai rejista ya yi daidai cewa sunan ba a so," Lauyan na SMUG, Edward Ssemambo, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Kotun daukaka kara da ta yanke wannan hukunci dai ta kasance kamar yadda kotun tsarin mulkin kasar ke sa ran nan ba da jimawa ba za ta yanke hukunci kan kalubalantar dokar hana luwadi, wadda ta shafi hukuncin kisa kan wasu laifukan jinsi guda da kuma hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.
An yi muhawara kan kalubalantar dokar a gaban kotu a watan Disamba. Masu rajin kare hakkin LGBT sun ce suna sa ran yanke hukunci nan ba da jimawa ba.
Ssemambo ya ce hukuncin na ranar Talata “bai mai da hankali ba ne” yayin da ake gabatowa hukuncin da za a yanke kan dokar da ta hana LGBT, ko da yake ya ce koken ya tabo batutuwan siyasa da na tattalin arziki da dama da za su iya yin la’akari da shawarwarin alkalan.
-Reuters