Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Slovenia Ta Yi Watsi da Auren Jinsi Daya


'Yan rajin auren jinsi daya suna jiran sakamakon zaben raba gaddama wanda daga bsani ya nuna kin amincewar al'ummar kasar da auren.
'Yan rajin auren jinsi daya suna jiran sakamakon zaben raba gaddama wanda daga bsani ya nuna kin amincewar al'ummar kasar da auren.

Masu kada kuri’a a zaben raba gardama a kasar Slovenia, sun bi sahun da yawa daga cikin takwarorinsu na kasashen kungiyar tarayyar turai, wajen kin amincewa da auren jinsa daya a kasar.

Kashi 63 cikin 100 na masu kada kuri’ar ne suka yi fatali da bukatar halalta auren masu luwadi da madugo, yayin da kashi 36 cikin 100 suka ce sun amince.

A farkon shekarar nan ne wasu ‘yan majalisu suka amince da wani kudirin doka kan halalta auren jinsi daya, sai dai wani gungun masu ra’ayin ‘yan mazan jiya da suka tattara sa hanun mutane, ya tilasta aka gudanar da zaben raba gardama.

Amma masu rajin a halalta auren mace da mace, ko kuma na miji da na miji, sun sha alwashin za su ci gaba da kokarin suga an amince da dokar a nan gaba, inda suka ce hakan kare hakkin bil adama ne.

Da zaben gardamar ya yi nasara, da kasar ta Slovenia ta zama kasa ta farko cikin tsoffin kasashen da suka bi tsarin kwamnisanci a baya, da ta amince da auren jinsi daya a nahiyar Turai.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG